Asabar 26 Yuli, 2025 da 4:04:26 Safiya
Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan tsakanin jam’iyyun hamayya inda suke nuna walle-walle da juna na jefa shakku a zukatan masu nazarin kimiyyar siyasa dangane da yiwuwar dunƙulewarsu wuri guda wajen ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a 2027.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma’a 26 ga watan Yulin 2025.
Asabar 26 Yuli, 2025 da 4:06:21 Safiya
Newcastle United ta kwaɗaitu da ɗan wasan Wolves’ mai shekara 25 daga Norway, Jorgen Strand Larsen.
Asabar 26 Yuli, 2025 da 4:03:15 Safiya
Rahotanni na nuna cewa hatta shugaban Amurka, babbar ƙawar Isra’ila, Donald Trump ya ƙule da Netanyahu bayan da Firaiministan na Isra’ila ya mamayi Amurka wajen kai hari a Syria, kan sabuwar gwamnatin da Trump ya amince da ita.
Asabar 26 Yuli, 2025 da 4:03:56 Safiya
Gwamnatin Birtaniya ta bayyana shirinta na rage tallafin ƙasashen waje, kuma tallafin karatun yara da na ilimin mata a Afirka ne ke fuskantar zaftarewa mafi girma.
Asabar 26 Yuli, 2025 da 6:43:20 Safiya
Yaƙin ya janyo asarar sama da mutum talatin da kuma dubbai da suka bar muhallinsu, tun bayan da rikicin kan iyakar ya ɓarke kwatsam ranar Alhamis.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma’a 25 ga watan Yulin 2025.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 6:09:48 Yamma
Chris ya ce bambancin addini ne ke jawo rikice-rikice, wanda a cewarsa ke jawo tashe-tashen hankula da kashe-kashe.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 12:13:35 Yamma
Hulk Hogan, ɗaya daga cikin mafiya shahara a wasan kokawa na reslin, ya mutu yana da shekara 71.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku sharhi da bayanan wasanni a faɗin duniya daga Asabar 19 - 25 ga watan Yulin 2025.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:01:17 Safiya
Liverpool na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Newcastle da Sweden, Alexander Isak mai shekara 25.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 12:45:10 Yamma
Abu na farko da mutum zai fara ji game da tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya shi ne ta lashe kofin ƙasashen Afirka sau tara, mafi yawa kenan a tarihin gasar.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 4:10:54 Safiya
Ɗanwasan Manchester City da Ingila Jack Grealish mai shekara 29, na cikin waɗanda Napoli ke zawarci.
Talata 22 Yuli, 2025 da 10:02:49 Yamma
Najeriya ta samu nasarar zura ƙwallo ta biyu gab da za a tashi wasa, lamarin da ya kawo ƙarshen mafarkin Afirka ta Kudu na kare kambinta, inda aka tashi Najeriya na da ci biyu Afirka ta Kudu kuma na da ɗaya.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:00:11 Safiya
A makon nan sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne yake ta faman amo a muhawara da tattaunawa a shafukan sada zumunta da ma a zahiri.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:11:57 Yamma
Sanarwar da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar ta ce: “rasuwar mai martaba babban rashi ne ga jihar Zamfara da ma daukacin arewacin Najeriya”.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:03:11 Safiya
'’Wace ce ADC? Me ya sa zan saki reshe in kama ganye? Su wane ne shugabannin haɗakar? Ba na cikin waɗanda ke biye wa mutane, a rufe ido a rufe tunani a yi ta hauka.’’
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:06:40 Safiya
Amurka da Isra’ila sun yi kakkausar suka ga matakin na Faransa, yayin da Saudiyya ta yaba da cewa tarihi ne, kamar yadda hukumomin Falasɗinawa suka yi maraba da shi.
Jummaʼa 25 Yuli, 2025 da 4:00:43 Safiya
Artabu tsakanin sojojin Thailand da Cambodia a kan iyakar ƙasashen da ake rikici a kai, ya janyo mutuwar mutum 12, a cewar hukumomin Thailand.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 9:57:31 Safiya
Kwamitin zartarwa na Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 6:32:23 Yamma
Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da yankin arewacin Najeriya, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 5:55:38 Yamma
Yin tattaki kafa 7,000 a kullum shi kaɗai yana ƙara wa kwakwalwa lafiya da kuma taimakawa mutum daga kamuwa da cututtuka daban-daban, kamar yadda wani bincike ya gano.
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 4:01:48 Safiya
'’Ina hango mana kan cewa idan ba mu kawo sababbin tsari da muka jawo mutane suka ci gaba da tafiya da APC ba, za mu fuskanci abin kunya a zabe mai zuwa - 2027.’’
Alhamis 24 Yuli, 2025 da 4:04:10 Safiya
Iko da yankin Kordofan mai arziƙin man fetur wata babbar nasara ce ga ƙungiyoyin da ke faɗa da juna a yunƙurinsu na ƙwace ƙasar, in ji manazarta.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 3:04:30 Yamma
A ranar Larabar nan ne ƴan majalisar dattawa guda huɗu da na wakilai guda uku suka sanar da sauya sheƙa daga jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa mai mulki ta APC.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/07/2025.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 4:57:40 Yamma
Shugaban Amurka Donald Trump ya kira yarjejeniyar da ya cimma da Japan a matsayin “ta cinikayya mafi girma a tarihi.”
__
Shafin bayani kai-tsaye kan binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 11:22:26 Safiya
Kundin tsarin mulkin Najeriya bai fayyace takamaimiyar rawa da sarakunan za su iya takawa ba, amma a baya-bayan nan zargin shiga harkar siyasa dumu-dumu da ake yi wa sarakunan ya haifar da saɓani da lalacewar dangantaka tsakaninsu da ƴansiyasa.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 4:01:04 Safiya
An kiyasta cewa kuɗin da mutanen ke da shi ya kai dala biliyan 57.4, sama da ɗaukacin duƙiyar ƴan Afirka miliyan 750, ko kuma rabin duƙiyar al’ummar nahiyar.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 2:39:54 Yamma
BBC ta ziyarci Babban Asibitin Kasa na Suweida, inda ma’aikatan asibitin suka yi ikirarin an kashe marasa lafiya a kan gadajensu.
Laraba 23 Yuli, 2025 da 4:01:52 Safiya
Aƙalla mutum biliyan ke cin shinkafa a duniya. Ana dafawa a gidaje a kullum, sannan an fi rabawa a bukukuwa.
Lahadi 13 Yuli, 2025 da 2:34:29 Yamma
Shin me ya sa aka ƙirƙiri hukumar? kuma mene ne ayyukanta?
Lahadi 13 Yuli, 2025 da 2:04:00 Yamma
Jihohin da rahoton ya lissafa su ne Borno da Yobe da Kano da Katsina da Sokoto da Neja da Benue, inda rahoton ya ƙara da cewa lamarin ya shafi kashi 63 cikin 100 na ƙananan hukumomin jihohin.
Asabar 12 Yuli, 2025 da 10:19:06 Safiya
Ya ce ya amince ya yi aiki da haɗakar ne a wani yunƙuri na kawar da gwamnatin Tinubun a babban zaɓen ƙasar mai zuwa.
Asabar 12 Yuli, 2025 da 8:21:07 Safiya
Lafiya Zinariya: Wane yanayi jikin mace ke shiga da ke janyo mata ciwon kai?
Lahadi 29 Yuni, 2025 da 11:29:40 Safiya
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu, shiri ne da BBC Hausa ke kawo muku labarai na ban dariya da nishaɗi, da ban al’ajabi a wasu lokutan ma har da ban taƙaici.